• 18 Jun, 2025

Matsin Lamba Na Daga Cikin Dalilan Da Suka Tilasta Ngelale Ya Fice Daga Gwamnatin Tinubu

Matsin Lamba Na Daga Cikin Dalilan Da Suka Tilasta Ngelale Ya Fice Daga Gwamnatin Tinubu

ajuri-1.jpg

Matsin lamba na daga cikin dalilan da suka tilasta mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu Ajuri Ngelale nisantar gwamnati.

Akwai kuma batun rashin tabbas da kin daukar shawara daga gwamnatin na Bola Tinubu wanda shi ma dalili ne da ya sanya Ngelale ya guji aiki a cikin ta.

Rahotannin sirri sun nuna cewa Ngelale baya goyon bayan abubuwan da ke faruwa a cikin gwamnatin kuma bai samu goyon baya daga wadanda suka dace ba.

A sakamakon haka ne Mai magana da yawun shugaban kasan Ajuri Ngelale ya yanke hukunci nisantar gwamnatin da dalilin rashin lafiyar iyalen sa.

Abin jiya a gani dai shi ne wanda zai maye gurbin Ngelale zai iya tafiya da gwamnatin ko kuwa ba zai iya ba.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.