• 18 Jun, 2025

Matatar Man Dangote Ta Garzaya Kotu Kan Yunkurin NNPCL Na Fara Shigowada Tataccen Mai Najeriya

Matatar Man Dangote Ta Garzaya Kotu Kan Yunkurin NNPCL Na Fara Shigowada Tataccen Mai Najeriya

1000004045.png

Matatar man Dangote ta garzaya kotu domin neman kotu ta dakatar da kamfanin mai na NNPCL fara shigo da tataccen mai Najeriya.

Gwamnatin kasar dai ta bawa kamfanin mai na NNPCL lasisin fara shigoda mai kasar duk da kasancewar matatar man Dangote ta fara aiki.

Matatar man na Dangote ta garzaya babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ta ke neman diyyar kudi Naira biliyan 100 daga hukunar da ke kula da harkar mai a kasar.

Kamfanin na Dangote ya ce hakan zai kawo mishi babban asara bayan makudan kudi da ya kashe don ganin matatar sa ta fara tace mai a kasa, amma kwatsam sai hukumar ta bawa NNPCL lasisin shigowa da tataccen mai kasar.

Saboda haka, matatar man na Dangote na neman kudi Naira biliyan 100 ne domin asarar da ke tunkarar ta.

Dangote ya ce hukumar kula da albarkatun man na kasa ta bawa kamfanin mai na NNPCL lasisi da kamfanin Matrix da sauransu domin su fara shigoda mai kasar musamman man fetur da man jirgin sama.

Matatar man na Dangote ta dauki lauyoyi wadanda lauya Ogwu Onoja ke jagoranta domin neman hakkinta a kotun ta tarayya.

Hukumar gudanarwa ta matatar man na Dangote ta ce ya zama dole ta nemi hakkinta a kotu domin jarin matatar na cikin hadari matukar NNPCL da sauran kamfanonin mai a kasar suka fara shigoda tataccen mai Najeriya.

Manaja a matatar man ta Dangote Ahmed Hashem ya ce dole ne suyi tsayin daka su tabbatarda kotu ta yi wani abu akan lamarin.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.