
Wasu fusatattun matasa sun karya manyan alluna da ke dauke da hotunan shugaba BolaTinubu da aka kafe a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
A jiya ne mataimakin shugaban kasan Kashim Shettima ya kai ziyarar aiki Damaturun don kaddamar da wani shirin tallafawa noma a jihar.
Minti daya zuwa biyar bayan mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da shirin, sai aka ga matasan na hawa kan manyan allunan suna lalata su, suna Allah wadai da mulkin Bola Tinubu.
An tsara shirin na gwamnatin tarayya ne don bunkasa noma da samar wa matasa Ayyukan yi a jihar ta Yobe.
Fusatan matasan dai na da nasaba da zanga-zangar da aka shirya yi a wata mai kamawa sakamakon wahalhalun tattalin arzikin kasa da jama'a ke ciki.