
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima da kakakin majalisar wakilai Abbas Tajudeen da mataimakin kakakin majalisa Benjamin Okezie Kalu na daga cikin jami'an gwamnati da su ka halarci taron shirya yara manyan gobe.
Kungiya mai zaman kanta ta CALDEV ce ta shirya toron, inda aka hada yara 300 daga sassan Najeriya domin ilmantar da su kan yadda za su gina soyayya ga kasar su, daga yanzu har zuwa lokacin da za su hau karagar mulkin kasar..
Yayinda wanda ya assasa kungiyar Bamidele Salam ke jawabi a wajen taron, ya bayyana cewa ranakun 17 da 21 ga wannan watan na daga cikin kwanakin da za a gudanar da taron a birnin tarayya Abuja.
Makasudin tara yaran dai shi ne kawo hadin kai tsakanin yaran da tabbatarda kishin kasa tsakanin yaran arewaci da kudanci da ma gabacin Najeriya baki daya.
Taron ya hada yara masu shekaru 12 zuwa 17, inda ganawan zai kara musu azama wajen dabarun mulki da fahimtar sarkakiyar da ke tattare da mulkin Najeriya.
Bamidele Salam ya ce, taron an shirya shi ne domin gano manyan gobe, ta hanyar bunkasa yaran dangane da abubuwan da ake bukata daga shugabannI.
Za a bawa yaran kyaututtuka musamman yaran da ke da fasaha cikin sauran yaran a fannonin rayuwa.
Daga cikin wadanda aka basu lambar yabo na kyaututtukan sun hada da wani yaro dan shekaru 10 mai suna Ashezi Akwashiki da Sheun Ayomide Samuel mai shekaru 16 da Maxwell Anyanwu dan shekaru 15 daga Lagas.