• 17 Jun, 2025

Masu Zanga-Zanga Sun Barke Da Sata A Kano

Masu Zanga-Zanga Sun Barke Da Sata A Kano

fb-img-17225120109143662.jpg

 

 

Masu zanga-zanga sun barke da satar kayan gwamnati a birnin Kano, arewa maso yammacin Najeriya.

Matasan kamar yadda hotuna suka nuna sun shiga wasu ofisoshin gwamnati inda suka wawure kujerun zama da na'urorin sanyaya daki da sauran kayayyaki.

Wasu daga cikin matasan sunce da kudaden su gwamnatoci ke sayan kayayyakin, don haka, sunada hakki a ciki.

Zanga-zangar dai an shirya shi ne na lumana domin kira ga gwamnati ta yi gyara cikin tsare-tsaren da ta bijiro da su domin yan kasa su samu sauki.

A yanzu dai zanga-zangar a Kano ta zama wani abu daban kamar yadda kuke gani.a hotuna.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.