Masu yiwa kasa hidama karkashin hukumar NYSC a Najeriya sun yi korafi gameda yadda har yanzu su ke karban Naira 33,000.
Matasan sun bayyana cewar suna fama da wahalhalu duba da yadda tsadar kayayyakin abinci da sauran kayayyakin rayuwa ya zama abin tsoro a Najeriya.
Matasan sun ce, duk da cewar gwamnatin tarayyar kasar ta yi shelar kara kudin kamar yadda ta kara albashin ma'aikatan kasar, kawo yanzu babu alamar karin kudin alawas din.
Gwamnatin Bola Tinubu dai ta ce ta kammala tsare-tsare domin duba kudin alawas din daga 33,000 zuwa 77,000 watanni biyu da suka gabata.
Gwamnatin tarayyar karkashin jagorancin shugaba Tinubu ba ta karawa matasan kudaden ba har watan nan na Nuwamba.
Kudaden alawas dai ana bawa matasa masu yiwa kasa hidima ne domin samun na sayan abincin sawa a baka.