
Gwamnatin Najeriya ta ce sama da yan Najeriya mutum dubu 22 da 500 ne ke dauke da takardun shaidar digirin boge a fadin kasar.
Ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya furta haka inda ya bayyana cewa shaidun karatun bogen duka na kasashen Benin da Togo ne da aka kammala daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Ministan ya ce masu dauke da takardun karatun boge dubu 21, 600 sun kammala karatun ne daga jami'ar kasar Benin, yayin da shaidun karatu 1,105 aka mallake su daga jami'ar kasar Togo inda duka gwamnatocin kasashen biyu ba su yarda da ingancin karatun ba.
Farfesa Tahir Mamman a wani ganawa da manema labarai ya bayyana cewa sun samu cikkakkun bayanan ne daga hukumar kula da yiwa kasa hidima NYSC da wasu kafafe da bai furta su ba.
Minsta Mamman ya ce akwai yiwuwar adadin masu dauke da shaidun takartun digirin bogen za su fi abinda aka gano kawo yanzu domin akwai wadanda ba sa yiwa kasa hidima ta yadda za a samu bayanan su.
Mamman ya ce hakan zai basu ciwon kai wajen zakulo su. Minista Tahir ya nuna takacin sa inda ya ce da dama daga cikin irin wadannan mutanen sunyi amfani da shaidun karatun bogen sun samu ayyuka a kasar.
Ministan ya kara da cewa irin wadannan mutanen sun samu ayyuka a ma'aikatun gwamnati da ma masu zaman kansu da sunan sunyi karatu, yayinda wadanda sukayi karatu mai nagarta suna zaune a gidajen su batare da sun samu ayyuka ba.