• 17 Jun, 2025

Masu Dakon Man Fetur A Najeriya Sun Sha Alwashin Fara Shigoda Mai Daga Kasashen Ketare Sakamakon Tsadar Litar Mai A Matatar Dangote

Masu Dakon Man Fetur A Najeriya Sun Sha Alwashin Fara Shigoda Mai Daga Kasashen Ketare Sakamakon Tsadar Litar Mai A Matatar Dangote

1000007582.jpg

Kungiyar masu dakon man fetur a Najeriya IPMAN, sun bayyana cewa sun kammala shirin fara shigowa da man fetur daga kasashen ketare.

Kungiyar sun ce farashin man daga kasashen waje da ma kudaden shigowa da shi ya fi sauki idan aka kwatanta da farashin man a Matatar man Dangote.

Kungiyar ta furta haka ne bayan bayanai da suka nuna cewa kudin litar man a matatar Dangote ya kai Naira 1,015 zuwa 10,28 kudin sari, inda Kungiyar ta ce ba za ta sabu ba bindiga a ruwa.

IPMAN ta ce tunda matatar man Dangote ta shiga harkar mai a Najeriya, ta jikita kudin litar man fetur a kasar.

IPMAN ta ce, akwai tazarar sauki da yawan gaske kan farashin man ferur daga kasashen ketare da yadda yake a matatar Dangote.

A nasa bangaren, sakataren masu gidajen mai a kasar Dakta Joseph Obeli ya ce, farashin litar man daga kasashen waje bai wuce Naira 800 akan kowani litar mai guda, inda ya bayyana cewa farashin ya fi na kamfanin man NNPCL da na Dangote sauki.

Obeli ya kara da cewa tuni sun rantaba hannu kan yarjejeniya da masu shigoda man fetur na kasa-da-kasa kan shirin fara shigoda tataccen man fetur Najeriya.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.