• 18 Jun, 2025

Masarautar Bauchi Ta Ci Zarafin Wani Sanata

Masarautar Bauchi Ta Ci Zarafin Wani Sanata

screenshot-20240815-141151-1723727543573.jpg

Masarautar a Bauchi ta kwace sunan girmamawa na sarautar gargajiya na dan majalisar dattawa Shehu Umar Buba.

An janye sunan majidadin Bauchi daga sanata Umar Buba ne sakamakon abinda masarautar ta kira nuna rashin da'a ga gwamnan jihar Bala Mohammed da sanatan ya yi.

Sanata Buba mai wakiltan Bauchi ta kudu a majalisar dattawan Najeriya a karkashin jam'iyya mai mulkin kasa ta APC ya rasa sunan girma na sarautar ta Bauchi bayan ya soki gwamna Mohammed.

Dan majalisan dattawan dai ya soki gwamna Bala Mohammed ne a maida martanin sa ga sukan shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnan yayi kan zanga-zangar da ta gabata.

Sanatan ya bayyana cewa shugaban kasa ba sa'an gwamnan ba ne, shi ne ya sa shi ma ya soki gwamnan Bala Mohammed.

Sanatan ya zargi gwamna Bala Mohammed da karkata kayan abinci da gwamnatin tarayya ta aika jihar da ma takin zamani domin bunkasa noma.

Mai bawa gwamna Bala Mohammed shawara kan harkar yada labaru Mukhtar Gidado ya ce ba su karkata kayayyakin ba kuma za su raba kamar yadda aka basu.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.