
Masana'antar shirya finafinai ta Kannywood a arewacin Najeriya na samun koma-baya a fagen taka-rawa a kasar da ma Afrika baki daya.
Wani mai sana'ar shirya finafinai a masana'antar Bollywood daga kudancin kasar Prince Daniel Aboki ne ya furta haka yayin gabatar da wani fim Mai suna Mai Martaba a fadar Sarkin Kano.
Aboki ya ce, a kalla Kamfanin NETFLIX ta kashe kudi Dala miliyan 175 a Najeriya da Kenya da Afrika ta Kudu don bunkasa harkar finafinai amma ko kobo masana'antar Kannywood ba ta samu ba.
Daniel Aboki ya ce, masana'antar Kannywood ba ta da kyakkyawar ginshiki da zai bata damar hada kafada da sauran masana'antun finafinan a fadin nahiyar Afrika.
Daniel ya ce, akwai bukatar a tallafawa masana'antar ta Kannywood wajen na'urorin zamani da karin masu basira a masana'antar.
Ya ce, fim din da aka shirya mai suna Mai Martaba shi ne mafi tsada da Kannywood ta taba yi.
Prince Daniel Aboki ya ce, a yanzu haka ana duba yiwuwar zaban fim din a daya daga cikin bukukuwa masu daraja a yankin turai wanda za'ayi a birnin Amsterdam dake kasar Netherlands.