
Wani malamin addinin Sheikh Bashar Danfili a jihar Sakkwato ya roki al-umma baki daya su taimake shi da kudade domin ceto iyalensa shida daga hannun 'yan bindiga.
'Yan bindigan sun yi garkuwa da iyalen malamin addinin Musuluncin ne a jihar Sakkwato, arewa maso yammacin Najeriya.
Anyi garkuwa da mahaifiyar malamin da kishiyar mahaifiyar tasa da matan sa biyu da 'yar uwarsa yayin da suke hanyarsu ta zuwa wani kauye.
'Yan bindigan sun kashe matukin motar da iyalen malamin ke ciki yayin tafiyar inda karnukan 'yan bindigan suka cinye naman sa.
Malam Bashar ya ce 'yan bindigan sun bukaci kudin fansa mai yawa daga gareshi wanda bazai iya biya ba kafin su sako iyalen nasa.
Malamin ya ce, yanzu haka wa'adin kwanakin da 'yan bindigan suka bada ya kusa karewa shi kuma baya maganin kobo ballantana miliyoyin kudi da suka bukata domin ceto iyalen sa.
Saboda haka, malam Bashar ya na rokon jama'a su mishi gudumawar kudi domin ceto iyalen sa daga hannun 'yan bindigan.