• 18 Jun, 2025

Malamin Addini Ya Shawarci Yan Najeriya Su Mallaki Makami Domin Kare Kansu

Malamin Addini Ya Shawarci Yan Najeriya Su Mallaki Makami Domin Kare Kansu

1724481136792.jpg

Wani sanannen malamin addinin musulunci Sheikh Bello Yabo yayi kira ga yan Najeriya su dauki matakin kare kansu da iyalen su sakamakon tabarbarewar tsaro a arewacin kasar.

Bello Yabo ya ce babu abinda ya saura a Najeriya face kowani dan kasan ya fara shirin kare kansa domin gwamnati ba za ta iya kare rayukan yan kasar ba.

Malam Yabo ya ce kowani dan Najeriya ya mallaki makamin kare kansa daidai da karfin sa duba da karuwar ta'addanci da gwamnatin kasar ta gaza tunkara sakamakon lalacewar shugabanci.

Sheikh Bello Yabo ya furta haka ne a maida martanin kan kisan gillar da yan bindiga suka yiwa Sarkin Gobir da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Malam Yabo ya ce ya zama dole kowa ya kare kansa. Wadanda ke da wadata su saya makamai, wadanda za su iya kerawa su yi hakan domin mallakar makaman kare kansu.

Muhammad Bello Yabo Ya ce abin takaici ne yan ta'adda su shiga gidan mutum su yi garkuwa da shi da matarsa don kawai suna rike da bindiga.

Bello Yabo ya kara da cewa tunda gwamnati tana samarwa yan ta'adda makamai dole ne mutane suma su nemi makamai domin kare rayukansu.

A makon nan ne dai yan bindiga suka kashe sarkin na Gobir Malam Bawa bayan sunyi garkuwa da shi sun bukaci kudin fansa har naira miliyan 60 da babura biyar kafin su sako shi.

A karshe dai yan bindigan suka kashe shi bayan angaza biya musu bukatun su kamar yadda suka ambata.

A baya dai yan bindigan sunyi garkuwa da dan Sarkin a watan Yuli a Kwanar Maharba yayin da yake kan hanyar sa zuwa gida daga birnin sokoto.

 

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.