
Babban daraktan asibitin kwararru na Jihar Taraba Alex Miangwa ya ce, mutane ba sa zuwa asibiti a wannan lokacin.
Miangwa ya bayyana cewa jama'an da su ke zuwa asibitin jinya sun ragu sosai idan aka kwatanta da lokutan baya.
Daraktan ya ce, matsin tattalin arzikin kasa baki daya, na daga cikin dalilan da su ka sa asibitin nasu ke fuskantar matsalar a wannan lokaci.
Babban daraktan ya furta haka ne yayinda ya ke zantawa da jaridar PREMIUM TIMES a babban birnin jihar Jalingo.
Daraktan ya bayyana cewa, talauci ne makasudin rashin samun mutane, inda mafi yawancin yan jihar su ka nemi wata mafita maimakon zuwa asibiti.
Miangwa ya kara da cewa, matsalar na shafan ayyukansu na yau da kullum, musamman harkar kiwon lafiya yadda ya kamata.
Miangwa ya ce, mutane da dama sun koma amfani da magungunan gargajiya sakamakon rashin kudi a hannayensu.
Miangwa ya kara da cewa, tsarin asusu guda ta TSA da gwamnatin jihar Taraba ta runguma, na daga cikin matsalolin da suka addabi cibiyar jinyar.
Babban daraktan asibitin kwararru ya ce, a baya asibitin nasu na samarwa cibiyar jinya ta tarayya wato FMC da ke jihar wasu daga cikin kayan aiki, amma sakamakon tsarin asusu guda, hakan ba ya yiwuwa a yanzu.