
Wani kwamitin majalisar wakilan Najeriya ya yi yunkurin hada kai da sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar da Shehun Borno Abubakar Ibn Umar da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta karatun tsangaya da maida hankali kan ilimin yara kanana a kasar.
Shugaban kwamitin majalisar Ibrahim Almustapha Aliyu ne ya nuna bukatar hakan yayin ziyarar da suka kai jihojin Sokoto da Borno da Yobe da Bauchi.
Ibrahim Almustapha mai wakiltar mazabar Wurno da Rabah a majalisar wakilan Najeeiya ya bayyana cewa ziyarar anyi ta ne domin karfafa niyyar kawo canji a harkar ilimin almajiranci da tunkarar matsalar yaran da basa zuwa makaranta.
A lokacin da kwamitin ke fadar shehun Borno, Ibrahim Almustapha ya yi cikakken bayani kan kokarin Shugaba Bola Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima domin inganta harkar ilimin wadanda ba su da gatan yin karatu a Najeriya.