• 18 Jun, 2025

Majalisa Za Ta Kafa Hukumar Zaben Kananan Hukumomi

Majalisa Za Ta Kafa Hukumar Zaben Kananan Hukumomi

Majalisa Za Ta Kafa Hukumar Zaben Kananan Hukumomi

gettyimages-1149349657-612x612.jpg

Majalisar dattawa za tayi dokar kafa wata hukumar zabe mai zaman kanta da za ta dauki dauyin gudanar da zaben kananan hukumoni 774 dake fadin Najeriya.

Shugaban kwamitin kula da harkokin kudade na majalisar tattawan sanata Sani Musa dan jam'iyyar APC daga jihar Naija shi ne ya gabatar da yunkurin dokar a zauren majalisar.

Idan majalisar dattawan tayi nasarar yin dokar kuma shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya hannu, hukumomin zabuka na jihohin kasar (SIECs) a takaice ba za su sake aiki ba.

Za'a kafa hukumar zaben ne domin daukar alhakin gudanar da zabukan kananan hukumomi 774 a fadin kasar cikin gaskiya da adalci kamar babbar hukumar zabe ta kasa (INEC).

Zabukan shugabannin kananan hukumoni da na gundumomi za su koma hannun sabuwar hukumar zaben ne idan majalisar ta cimma nasarar kafa ta.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.