
A kalla mutum hudu sun rasa rayukansu a wani hari da aka kai a wani yanki a jihar Filato, arewa maso tsakiyar Najeriya.
Shugaban kungiyar matasan Butura, Sabastine Majit, ya tabbatar da faruwar harin a Jos, a ranar Asabar.
Ya bayyana sunayen wadanda aka kashe kamar Bwefuk Musa, Klingshak Dickson, Promise Joshua da Nyam Abaka.
Ya kuma kara da cewa wadanda suka kai harin sun gudu kafin zuwan jami’an tsaro.
Majit ya ce idan hukumomi ba su dauki matakin kawo ƙarshen hare-haren ba, al’ummar yankin za su dauki makamai don kare kansu.
Majit, ya bayyana cewa wannan hari ya faru ne kwanaki hudu bayan aukuwar wani mummunan al’amari a kauyen Wumat, inda aka kashe mutane biyar ‘yan gida faya, ciki har da wata mata mai juna biyu.
Ya kara da cewa a cikin wata daya da ya gabata, an kashe sama da mutum 20 a yankinsu a sanadin hare-haren da ba a san dalilinsu ba.