• 18 Jun, 2025

Mace Ta Farko Ta Zama Shugabar Jami'ar Nnamdi Azikiwe

Mace Ta Farko Ta Zama Shugabar Jami'ar Nnamdi Azikiwe

Mace Ta Farko Ta Zama Shugabar Jami'ar Nnamdi Azikiwe

carol-arinze-umobi.jpg

A karon farko mace ta zama shugabar jami'ar tarayya UNIZIK dake birnin Awka a jihar Anambra.

Farfesa Carol Arinze-Umobi za ta hau kujerar shugabancin jami'ar bayan tayi nasarar cin jarabawar shiga ofishin.

Shugaban gudanar wa na jami'ar Ambassador Gregory Mbadiwe ne ya sanar da hakan jiya a Awka.

Shugaban ya ce, Carol za ta jagoranci jami'ar  na tsawon watanni shida a matsayin mai rikon kwarya kamar yadda dokar jami'ar Act CAP 139 LFN ta tanada.

Carol Arinze-Umobi za ta fara aikin shugabancin Jami'ar gobe Litini 22 ga wannan watan.

Farfesa Arinze Umobi tsohuwar mataimakiyar shugaban jami'ar ce a baya, kuma ta goge a fannin Shari'a, musamman bangaren kare hakkin bil'adama.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.