• 17 Jun, 2025

Kungiyar Yarbawa Ta Gargadi Shugaba Tinubu Dangane Da Kabilanci Da Ya Ke Yi Wajen Raba Mukaman Gwamnatin Tarayya

Kungiyar Yarbawa Ta Gargadi Shugaba Tinubu Dangane Da Kabilanci Da Ya Ke Yi Wajen Raba Mukaman Gwamnatin Tarayya

1000007795.jpg

Kungiyar kabilar Yarbawa a Najeriya ta gargadi Shugaba Bola Tinubu dangane da son kai da ya ke yi wajen bada mukamai a gwamnatinsa.

Kungiyar ta Afenifere ta ce Bola Tinubu ya dora kabilar Yarbawa sama da kowa wajen manyan mukaman gwamnatin tarayyar Najeriya.

Afenifere ta furta hakan ne a wata takarda da ta fitar mai dauke da sa hannun sakatarorin yada labaranta Ayo Adebanjo da Faleye a birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

Afenifere ta ce, halin Bola Tinubu ka iya janyo barazanar dangantaka da ke tsakanin kabilun Najeriya matukar shugaban bai canja salon sa ba.

Kungiyar ta ce, ba za ta lamunci tsagwaron banbanci da sbugaban kasa ke nunawa ba, inda yake bawa Yarbawa manyan mukaman kasar.

Afenifere ta ce, shugaban hukuman tsaro na sirri DSS da hukumar yaki da zagon kasa na EFCC da ministan Shari'a da ministan kudi da ma gwamnan babban bankin kasar da shugaban sojan kasa da na yan'sanda da na fasakwori da sauransu duk yan kabilar Yarbawa ne.

Kungiyar ta ce hakan son kai ne karara kuma ba za ta goyi bayan abinda Tinubu ke yi akan kabilar Fulani a arewacin Najeriya ba, bayan dangantakar siyasa da ke tsakani shekara aru-aru.

Afenifere ta ce, duk da cewar an zargi tsohon shugaban kasa Buhari da yin banbanci wajen bada mukamai, amma na Bola Tinubu ya yi muni kuma ya zama dole ya kawo karshen hakan kafin lokaci ya kure mishi.

Akarshe, Afenifere ta ce, babu banbancin kabila a manufofin kungiyar kamar yadda jagoran kabilar Yarbawa Obafemi Awolowo ya shinfida a kundin kungiyar Afenifere.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.