
Masu dakon man fetur a Najeriya sunyi korafin dogagen layuka a kamfanin man Dangote batare da samun mai ba.
Yan kasuwan karkashin kungiyar IPMAN sun bayyana cewa sun shafe kwanaki suna kan layi amma ba a loda wa tankokinsu mai ba.
Shugaban IPMAN Abubakar Garima ya bayyana haka ne yayinda ya ke tattaunawa da tashar talabijin na Channels jiya Laraba.
Garima yana mamakin korafin da Aliko Dangote ya kebyi dangane da shigo da tataccen mai Najeriya, yayinda ya gaza samarda man a gida.
Shugaban na IPMAN ya ce babu wani dan kungiyar da ya ke shigoda mai daga kasashen ketare kamar yadda Dangote ke ikrari.
Shugaban IPMAN ya ce suma suna bukatar sayan man daga kamfanin Dangote kai tsaye maimakon biya ta hannun kamfanin man NNPCL.
Abubakar ya ce, yanzu haka akwai kudin kungiyar a hannun kamfanin mai na NNPCL har Naira biliyan 40 amma har yanzu ba su samu man ba.
Abubakar ya kara da cewa akwai wasu daga cikin yan kungiyar ta IPMAN da suka shafe kwanaki 4 amma ba su samu mai a kamfanin na Dangote ba, bayan NNPCL ya bada umarni a basu man.