
Kungiyar malaman jami'a ASUU reshen jami'ar Abuja ta bukaci yin adalci cikin zaben sabon shugaban jami'ar na gaba, yayinda mutane 18 ke neman kujerar jagorantar jami'ar.
Kungiyar ta ja hankalin hukumar gudanarwa ta jami'ar da ta tabbatarda adalci ga kowani dan takarar da ke neman kujerar ta hanyar bin ka'idojin da jami'a ta gindaya.
Yayinda ya ke zantawa da 'yan jaridu, Shugaban kungiyar ta ASUU reshen jami'ar Abuja Dakta Sylvanus Ugoh ya ce su na da kwarin gwiwar za a bi ka'idojin zaben.
Kungiyar ta bayyana cewa ba za ta sa baki a cikin harkar zaben shugaban ba, kuma ba ta da wani dan takara da take so ya yi nasarar zama shugaban jami'ar.
Bukatar kungiyar ta bakin Dakta Ugoh ita ce gudanarda zabe cikin 'yanci da walwala ba tare da ha'inci da son kai ba.
Dakta Ugoh ya ce akwai bukatar hukumar gudanarwar jami'ar ta Abuja ta mutunta dokoki da ka'idojin zaben shugaban jami'ar domin mutuncin jami'ar a idon duniya, duba da kaurin sunan da jami'ar ta yi wajen rashawa.
Kungiyar ta kara da cewa, dukkan masu neman kujerar shugabancin jami'ar 'yan kungiyar ASUU ne, don haka, babu bukatar magudi, domin duk wanda ya yi nasara su na tare da shi.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar gudanarwar jami'ar na samun matsin lamba, inda ake bukatar ta gudanarda zabe mai nagarta ba tare da wani ya karkata akalar zaben ba.
A nata bangaren, hukumar gudanarwa ta jami'ar ta yi alkawarin gudanarda zabe mai nagarta ta hanyar bin dukkan tanade-tanaden dukar zaben shugaban jami'ar.