• 17 Jun, 2025

Kungiyar Kwadagon Najeriya Ta Amince Da Mafi Kankancin Albashi Naira Dubu...

Kungiyar Kwadagon Najeriya Ta Amince Da Mafi Kankancin Albashi Naira Dubu...

Kungiyar Kwadagon Najeriya Ta Amince Da Mafi Kankancin Albashi Naira Dubu...

screenshot-20240719-160434-1721403545860.jpg

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC, ta bada dalilan ta na amincewa da mafi kankancin albashin ma'aikaci Naira dubu 70,000.

Kungiyar ta furta hakan ne bayan wakilan ta sun gana da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya ta Aso Rock Villa a Abuja.

Kungiyar ta ce, dalilan ta na amincewa da Naira 70,000 sun hada da matsin tattalin arzikin da gwamnatin Najeriya ke fuskanta da ma duniya baki daya.

Kungiyar ta ambaci wahalhalu da 'yan Najeriya ke ciki na talauci da rashin tabbas a matsayin dalili na biyu da ya tilasta mata amincewa da mafi kankancin albashin na Naira 70,000.

Kungiyar ta ce, idan ba ta amince da Naira dubu saba'in din ba, batasan yaushe za ta kammala yarjejeniyar albashin da gwamnati ba, yayin da talaka shi ne mai shan wahala tsawon lokacin yarjejeniyar.

Kungiyar ta bakin Shugaban ta, ta ce, wadannan na daga cikin manyan dalilan da suka tilasta ta mika wuya ga bukatar gwamnatin tarayya na Naira 70,000.

Kungiyar ta ce, a baya ta dage kan mafi kankancin albashin ma'aikaci Naira 615,000, sa'annan ta sauko zuwa 250,000.

A karshe dai kungiyar ta mika wuya ga abinda gwamnatin Najeriya ta bada, inda ta amince da kudi Naira 70,000 a zaman mafi kankancin albashin da karamin ma'aikaci a kasar zai rika karba a kowani wata.