• 17 Jun, 2025

Kungiyar Kare Hakkin Dan'adam Ta Umarci Gwamnatin Najeriya Da Ta Saki Kananan Yara Da Aka Gurfanar A Kotu Jiya

Kungiyar Kare Hakkin Dan'adam Ta Umarci Gwamnatin Najeriya Da Ta Saki Kananan Yara Da Aka Gurfanar A Kotu Jiya

1000007643.jpg

Kungiyar kare hakkin dan'adam ta Amnesty International ta ce dole ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya saki dukkanin wadanda aka kama a kan zanga-zangar tsadar rayuwa.

Da yake martani kan batun komawa shari'ar masu zanga-zangar da aka yi a wata babbar kotun tarayya jiya a Abuja.

Darektan kungiyar a Najeriya Isa Sanusi, ya ce dole ne shugaban kasar ya saki dukkanin wadanda aka kama a kan zanga-zangar kuma ba tare da wani sharadi ba.

Ya ce tsare mutanen tun watan Agusta saboda kawai sun yi amfani da dama da 'yancinsu na zanga-zangar lumana tare da tuhumarsu da laifuka na ban mamaki da suka hada da cin amanar kasa da ta'addanci ya nuna yadda gwamnatin Najeriya ba ta mutunta 'yancin ɗan'Adam.

Darektan ya ce masu zanga-zangar 114 da aka gurfanar a kotun ba su yi wani abu da ya saba doka ba, kuma ba su cancanci irin muzgunawar da aka yi musu ba tun daga lokacin da aka kama su

Ya ce daga cikin mutum 76 da aka fara gabatarwa a kotun a jiya, yawancinsu yara ne, kuma faduwar hudu daga cikinsu a kotu alama ce da ta nuna mummunan yanayin da lafiyarsu ke ciki.

Shugaban kungiyar ta Amnesty ya ce tsare yara a irin wannan yanayi na tashin hankali a kan kin amincewarsu tare da neman mulki na gari ya nuna kudurin gwamnati na murkushe masu suka.

Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce zai yi wa yara akalla ,iliyan 3.8 allurar riga-kafin kyanda a wasu jihohi hudu na arewacin Najeriya.

Babban jami'in lafiya na hukumar ta UNICEF a Bauchi, Patrick Akor, shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai jiya Juma'a a Bauchi, inda ya je a yau Asabar za a fara allurar da za a yi tsawon kwana bakwai.

Jami'in ya ce jihohin da za a yi wa yara, 'yan kusan shekara biyar zuwa shekara tara allurar su ne Adamawa da Bauchi da Gombe da kuma Filato.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.