• 17 Jun, 2025

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama Ta Gardadi Gwamnatin Najeriya

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama Ta Gardadi Gwamnatin Najeriya

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama Ta Gardadi Gwamnatin Najeriya

screenshot-20240729-080500-1722236737193-1722236758960.jpg

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa-da-kasa ta yi gargadi cewa yin barazana ga masu shirin gudanar da zanga-zanga cin muruncin dimokuradiyya ne.

Shirin zanga-zangar da za'a fara daga ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa, ta samu karbuwa a shafukan sada zumunta da kuma wasu ‘yan kasar.

Hukumomin Najeriya sun yi gargadi kan gudanar da zanga-zangar da za ta jefa kasar cikin tashin hankali kamar yadda wasu  kasashe a Afrika suka shiga a baya.

Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta ce yan kasar na da 'yancin yin zanga-zanga ta lumana, amma mahukuntan kasar basason yin hakan domin suna ta yunkurin ganin sun dakile ta.

Kungiyar tace zanga-zanga tana daya daga cikin tsarin mulkin dimokuradiyya da muke ciki domin ko shugaban kasa na yanzu ya taba yin zanga-zangar a Najeriya.

Kungiyar tace, yi wa masu zanga-zangar barazana, zai kawo koma baya ga mulkin dimokuradiyya a kasar.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.