
Kungiyar Dattawan Arewa wato Arewa Consultative Forum a Turance, ta bayyana tabarbarewar tattalin arzikin yankin arewa, sakamakon tsare-tsare marasa kan gado da Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar.
Kungiyar ta nuna damuwa dangane da hakan, inda ta ce, akwai matsaloli da dama da 'yan arewa ke fuskanta a jagorancin shugaba Bola Tinubu.
Kungiyar ta ce, akwai matsalar rashin zuwa makaranta daga bangaren yara kanana, wanda hakan babban komabaya ne ga yankin mai dunbun albarkatun kasa da yawan al-umma.
Gamayyar dattawan sun yi kira ga Shugaban kasa ya dauki matakan kawo canji ta fuskar rashin tsaro, da matsin tattalin arziki da harkar ilimi, musamman ilimin yara kanana a arewacin kasar.
Kungiyar ta furta haka ne a wata takarda ta ta fitar, wanda Sakataren yada labarunta Farfesa Tukur Muhammad Baba ya sanyawa hannu, bayan wata ganawa da ta yi da masu ruwa da tsaki na kungiyar, jiya Laraba a birnin Kaduna.
ACF ta ce, yankin arewa na fama da barazanar zaman lafiya wadanda suka hada da ta'addanci, da garkuwa da mutane da sauransu.
Kungiyar ta kara da cewa, akwai bukatar shugaban kasa Bola Tinubu ya sake duba tsare-tsaren sa na tattalin arzikin kasa, domin babu wani alfanu ko kadan da tsare-tsaren su ka haifar.