
Ministan tsaron Najeriya Muhammad Badaru ya umarci rundunar Fansar Yamma ta sojojin kasar da su farauto mishi babban dan bindigan nan Bello Turji batare da bata lokaci ba.
Ministan ya daukin matakin ne awa 24 bayan tsallake kora da shugaba kasa Ahmed Bola Tinubu ya yi wa wasu ministocin sa jiya Laraba.
Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Ananuga ya bayyana dalilan da suka sa shugaba Bola Tinubu bai kori Matawalle daga kujerar ministan tsaron ba.
Yayinda ya ke ganawa da rundunar sojojin kasar ta birget na 1 da ke Gusau jigar Zamfara yau Alhamis, ministan ya karawa sojojin karfin gwiwa inda ya ce, shugaban kasa ya gamsu da kokarin da su ke yi cikin watannin da suka gabata.
Ministan ya shaidawa sojojin cewa shugaba Tinubu ya yaba aikin su kuma akwai bukatar sojojin su kara himma kan aikin tsaron kasar.
Ministan ya kara da cewa shugaban kasa zai bawa sojojin dukkan abubuwan da suke bukata domin kawo karshen rashin tsaro a arewa maso yammacin Najeriya.
Ministan ya ce, gwamnatin tarayya na shirye domin kawo karshen Bello Turji da dukkan yan bindiga a yankin.
Yau sati uku kenan bayan shugaban rundunar tsaro na sojan kasar Janar Christopher Musa ya yi alwashin kawo karshen babban dan bindigan Bello Turji.
Christopher Musa ya kara da cewa ayyukan murkushe yan bindiga da sojojin Najeriya ke yi ya jefa tsoro cikin zuciyar Bello Turji da ma yaran sa.