• 17 Jun, 2025

Ku Guji Nuna Kabilanci A Ayyukan Ku Na Ministocin Kasa—Cewar Sakataren Tarayya Akume

Ku Guji Nuna Kabilanci A Ayyukan Ku Na Ministocin Kasa—Cewar Sakataren Tarayya Akume

1000008930.jpg

Gwamnatin Najeriya ta gargadi ministoci da su kiyayi akidar nuna kabilanci wajen gudanarda ayyukansu a matsayinsu na ministocin kasa baki daya, domin kawo cigaba a Najeriya.

Sakataren gwamnatin tarayya Sanata Geoge Akume ne ya furta gargadin a jiya Alhamis a Abuja yayin wani taro na kwanaki biyu da ofishinsa ya shirya don ilmantarda manyan ma'aikata.

Sakataren tarayyar Akume, ya ja hankalin ministocin da su girmama muradun kasa ba son zuciyarsu ba, inda ya ce, an basu mukaman ne domin kawo sauyi mai ma'ana ba son kai ba.

Akume ya ce, shugaban kasa Bola Tinubu ya hau karagar mulki ne domin hadin kan kasa da ci gaba, ba don banbance-banceba.

Akume ya kara da cewa Tinubu na da zummar kawo sauyi ta fannonin tattalin arzikin kasa da ababen more rayuwa da sauran abubuwa masu ma'ana a Najeriya.

Geoge Akume ya ce, ya zama wajibi ministocin su rungumi manufofin gwamnatin tarayya karkashin shugaba Bola Tinubu domin ci da kasar gaba.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.