• 18 Jun, 2025

Kotun Kolin Najeriya Za Ta Taimaka Wajen Yaki Da Rashawa—Cewar Kudirat Kekere

Kotun Kolin Najeriya Za Ta Taimaka Wajen Yaki Da Rashawa—Cewar Kudirat Kekere

1000002547.jpg

Babbar mai Shari'a a kotun kolin Najeriya Kudirat Kekere-Ekun ta ce bangaren Shari'a na shirye domin bada gudumawar kawo sauyi a kasar.

Kekere-Ekun ta furta haka ne yayinda tayi jawabi a taron yaki da rashawa karo na 37 da aka gudanar a birnin Uyo da ke jihar Akwa Ibom, kudu maso kudancin Najeriya.

Taron na karawa juna sani an gudanar dashi ne don fahimtar kalubale da bangaren Shari'a ke fiskanta a kasar tare da gabatarda shawarwari don cimma nasara.

Kudirat wacce mai Shari'a Adamu Ajeoro na kotun koli ya wakilta ta ce bangaren shari'ar kasar ya shirya tsaf don hadin wajen kawo sauyi a Najeriya.

A nasa bangaren, shugaban Hukumar da ta shirya taron Olanrewaju Suraju ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda bangaren Shari'a a Najeriya ya lalace da rashawa, inda ya ce dole ne sai yan kasar sun tashi tsaye kan batun na rashawa da ke dab da rushe kasar baki daya.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.