• 18 Jun, 2025

Kotu Tayi Watsi Da Bukatar Wasu Kamfanoni A Kano

Kotu Tayi Watsi Da Bukatar Wasu Kamfanoni A Kano

Kotu Tayi Watsi Da Bukatar Wasu Kamfanoni A Kano

screenshot-20240723-110242-1721728987073-1721729027112-1.jpg

Kotun tarayya a birnin Kano ta yi watsi da karar da wasu kamfanoni suka shigar don neman ta dakatar da kamfanin wutar lantarki kara musu kudin wutar.

A watan hudu ne wasu masana'antu suka shigar da korafin gaban kotun sakamakon Karin kudin wuta ga wadanda ke rukunin "A."

Kamfanin wutar ta KEDCO tare da hukumar wutar lantarki ta kasa NERC sun kara kudin wutar ne sakamakon karuwar ayyukan kula da wutar a Najeriya.

Mai Shari'a Simon A. Amobeda ya ce, kamfanonin basuda hurumin dakatar da karin wutar lantarkin domin anyi shi ne bisa dokar kasa.

Amobeda ya ce, karin kudin wutar na daidai da kundin tsarin mulkin Najeriya na 116 sakin layi na 6,7,8,9 da 10 na dokar da ta kafa hukumar kula da wutar lantarki ta kasa.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.