• 17 Jun, 2025

Kotu A Ibadan Ta Yi Watsi Da Karar Da Aka Shigar Kan 'Yancinn Sa Hijabi A Makaranta

Kotu A Ibadan Ta Yi Watsi Da Karar Da Aka Shigar Kan 'Yancinn Sa Hijabi A Makaranta

1000010154.jpg

Babbar kotun jihar Oyo da ke birnin Ibadan a kudu maso yammacin Najeriya ta yi watsi da karar da makarantan sakandaren jami'ar Ibadan ta shigar a gabanta.

Makarantar sakandaren dai ta yi karar jami'ar Ibadan ne kan rigimar ko dalibai mata Musulmai na sakandaren na da 'yancin sanya hijabi ko akasin haka.

Alkalin kotun Moshood Ishola wanda ya yanke hukuncin ya bayyana cewa babbar kotun jihar ba ta da hurumin sauraron karar, saboda tuni an daukaka ta zuwa kotun daukaka kara ta tarayya.

Ishola ya ce, sauraron karar karya dokar Shari'a ne tunda karar na hannun kotun daukaka kara ta tarayya, wanda ya zama dole a jira hukuncinta kan batun.

Alkalin Kotun Ishola ya ce rashin girmama kotu ne idan ya saurari karar batare da umarnin kotun tarayyar ba.

Abin jira a gani dai shi ne yadda za ta kaya a kotun daukaka kara ta tarayya kan batun sanya hijabin mata Musulmai a makarantar ta Ibadan, inda a dokar kasa matan na da 'yancin gudanar da addininsu cikin walwala.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.