• 17 Jun, 2025

Ko Yaya Donald Trump Zai Gudanarda Mulkinsa Karo Na Biyu A Kasar Amurka?

Ko Yaya Donald Trump Zai Gudanarda Mulkinsa Karo Na Biyu A Kasar Amurka?

1000008710.jpg

Sabon Zababben shugaban kasae Amurka Donald Trump na daga cikin shugabannin kasar masu matukar sa'a, domin ba karamin aiki ba ne mutum ya fadi zaben neman wa'adi na biyu a Amurka, kuma ya sake samun wata damar bayan shekaru hudu.

Komawar Donald Trump fadar Shugaban kasar Amurkan na nuna shirin sake fasalin manufofin Amurka ta fannin ma'amalarta da sauran kasashen duniya, inda ake tunanin za a sama wasu sauye-sauye da dama a lokacin da yake-yake ke damun wasu kasashen duniya.

A lokacin yakin neman zaben Donald Trump, ya yi alkawurran manufofin siyasa ba tare da yin cikakken bayani ba, inda da ya yi ikirarin dawo da martabar Amurka ta hanyar daukaka kasar Amirka sama da komai.

Nasarar da ya yi tana nunin da cewa cikin manyan abubuwan da za su iya kawo cikas a mulkinsa ta fannin harkokin kasashen ketare, yayin da ake fama da rigingimu a fadin duniya.

Abin tambayan shi ne, ko mutanen duniya za su iya hasashen matakan da shugaba Trump zai iya dauka a sassan duniya duba da irin.kalamansa yayin yakin neman zabe da tarihinsa mulkinsa na baya?

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.