• 17 Jun, 2025

Kayan Abinci Ya Fara Tashin Gwauron Zabi A Wasu Jihohin Arewa Sakamakon Rashin Wutar Lantarki

Kayan Abinci Ya Fara Tashin Gwauron Zabi A Wasu Jihohin Arewa Sakamakon Rashin Wutar Lantarki

1000006267.jpg

Sakamakon rashin wutar lantarki a arewacin Najeriya, kudaden kayayyakin abinci sun fara tashin gwauron zabi.

Farashin abinci kamar shinkafa da kudin ruwa da kiwon lafiya da sauran ababan more rayuwa sun fara ta'azzara a jihohin arewa a kowace rana.

A jihohin Jigawa da Gombe da Bauchi, buhun shinkafa yar gida ta kai kudi Naira 150, 000 zuwa 160,000, inda a baya bai kai haka ba.

Masu harkar sarrafa shinkafa sun nuna damuwa kan yanayin, inda suka bayyana cewa idan ba a yi wani abu akan rashin wutar lantarki ba, akwai babbar matsala.

Sakamakon rashin wutar da tsadar man fetur ne suka haddasa tsadar abincin da sauran kayayyakin yau da kullum da mutane ke amfani da su.

Masu sarrafa shinkafar sun ce suna amfani ne da inji don samun wutar da bata taka kara ta karya ba, bayan tsadar kudin mai.

Akwai alamun karin farashin duk wani kayan masarufi da ake amfani da shi idan aka cigaba da fuskantar matsalar rashin wutar.

Gawayi ma da mutane ke amfani da shi wajen girki yayi tsada fiye da yadda ake tunani sabanin yadda ake samun shi a baya.

Akwai bukatar jihohin kasar su duba yiwuwar samarda wutar lantarki na kansu kamar yadda tuni wasu jihohin kamar Jigawa da sauransu suka fara yin dokoki domin hakan.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.