• 18 Jun, 2025

Kashim Shettima Da Abbas Tajudeen Sun Gana Kan Ambaliyar Maiduguri

Kashim Shettima Da Abbas Tajudeen Sun Gana Kan Ambaliyar Maiduguri

fb-img-17261332365536366.jpg

Mataimakin Shugaban kasan Najeriya Kashim Shettima da kakakin majalisar wakilan kasar sun hada kai domin tunkarar matsalar ambaliya a jihar Borno da sauran jihohin kasar.

Kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya gana da Kashim Shettima ne a fadar Shugaban kasa da ke Abuja domin tattauna mafitar ambaliyar da ta ritsa da birnin Maiduguri.

Tajudeen Abbas ya jajanta wa mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima wanda dan jihar Borno ne game da iftila'in ambaliyar, inda ya ce za su duba hanyar da za su taimakawa al-ummar ta Borno.

Tuni dai Shugaba Bola Tinubu umarci hukumar agajin gaggawa ta NEMA su fara aiki   na musamman domin taimakawa wadanda masifar ambaliyar ta shafa.

Bayan ganawa da mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, Tajudeen Abbas ya shaidawa manema labarai cewa sun tattauna yadda za su fitowa lamarin ambaliyar ta Maiduguri.

Abbas ya ce gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 3 domin aikin tallafawa 'yan Maiduguri da ambaliyar ruwan ta shafa.

Kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya kara da cewa akwai wasu jihohin kasar kamar irin  Kaduna da Naija da sauran su da ke fama da matsalar ambaliya da Majalisar wakilan za ta taimakawa.o

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.