• 17 Jun, 2025

Kashi 2 Cikin 3 Na 'Yan Najeriya Ba Sa Iya Sayen Abinci Mai Lafiya—Cewar Hukumar Kididdiga Ta NBS

Kashi 2 Cikin 3 Na 'Yan Najeriya Ba Sa Iya Sayen Abinci Mai Lafiya—Cewar Hukumar Kididdiga Ta NBS

1000012843.jpg

Wani bincike da hukumar kididdiga ta NBS a Najeriya ta gudanar, ya nuna cewa kashi biyu cikin uku na 'yan Najeriya basu da kudin sayen lafiyayyen abinci.

Binciken ya kuma gano cewa iyalai a kasar na fuskantar kaso 6.7 na daukewar hasken lantarki a kowani mako sakamakon rashin tabbas na wutar ta lantarki.

Binciken ya yi nazarin matsanancin talauci dake addabar 'yan kasar da kuma tasirin hakan ga 'yan Najeriya, inda ba sa iya sayen kayan masarufin da suke bukata saboda matsalar hauhawar farashi su a kasuwa.

Da dama daga cikin magidanta a binciken da aka yi, sun bayyana gazawarsu wajen iya cin lafiyayyen abinci mai gina jiki ko kuma irin wanda ransu ke so saboda rashin kudade a hannunsu.

Haka kuma  kaso 68.3 cikin 100 na magidantan na iya cin nau’uka kalilan ne na kayan abinci saboda matsalar rashin kudade, inda kaso 62.4 na nuna damuwa kan rashin wadatar abincin da za su ci baki daya. Binciken na hukumar kididdigar kasar ya bankado karin abubuwa da dama bayan wadannan.

Masana da dama sun ce, matsin tattalin arziki da ke addabar kasar ce ke shafar al-umma, sakamakon tsare-tsare da gwamnatin kasar karkashin shugaba Bola Tinubu ta bijiro da su.

Rashin darajar kudin Najeriya ta Naira da cire tallafin man fetur na daga cikin manyan dalilan da suka jefa 'yan kasar cikin wahalhalu a cewar masana tattalin arzikin kasa, inda su ka ce ya zama dole gwamnatin kasar tayi gaggawar daukan mataki kafin lamarin ya rincabe baki daya.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.