• 18 Jun, 2025

Kasar Chana Ta Kwace Wasu Gidaje A Birnin Liverpool Mallakar Najeriya

Kasar Chana Ta Kwace Wasu Gidaje A Birnin Liverpool Mallakar Najeriya

img-7329-1-1.jpeg

A ci gaba da rigima tsakanin Najeriya da kasar Chana bayan umarnin kotu, kamfanin kasar Chana ta kwace wasu gidaje mallakar Najeriya na Dalolin miliyoyi a birnin Liverpool da ke kasar Ingila.

Kamfanin na Kasar Chana Zhongshang Fucheng Industrial Investment Limited 
ya dauki matakin ne a kokarin sa na rage asara kan ragowar kudin da ya ke bin Najeriya har Dalar Amurka miliyan 70.

Kamfanin ya ce matakin ya zama dole biyo bayan nuna halin ko-in-kula da Najeriya ta yi wajen biyan basukan sakamakon hukuncin kotu na shekara 2021.

Kamfanin ya kwace gida mai lamba 15 Aigburth Hall Road da gida mai lamba 49 Beech lodge a Calderstones road duka a birnin na Liverpool da ke kasar Ingila a watan Yunin wannan shekarar.

Kamfanin na kasar Chana dai ya yi ikrarin karya ka'idojin yarjejeniya da Jihar Ogun ta yi a shekarar 2016.

Kan hakane kamfanin ya maka gwamnatin Najeriya a wata kotun kasar Ingila a shekara ta 2018 cewar gwamnatin Najeriya tayi amfani da jami'an yan sandan ta da ma na shige-da-ficen Najeriyar ba tare da bin ka'ida ba.

Kasar Chanan ta ce, gwamnatin Najeriya ta ci zarafin dan kasar ta ta hanyar tsare shi da ma yi wa wani korar kare duk da ba su da wani laifi a batun.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.