
Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da karin harajin VAT daga kashi 7.5 cikin dari zuwa kashi 10 cikin dari.
Atiku ya bayyana karin kudin haraji kan kayayyakin masarufi a matsayin babban masifa da ke kama da gobara da ka iya cinye 'yan Najeriya baki daya.
Abubakar ya ce wannan halin na shugaba Tinubu ya nuna karara gwamnatin sa ba gwamnati ce mai tausayin talaka ba, gwamnati ce da ta zo domin tsare-tsaren jefa 'yan Najeriya cikin karin masufu kan wadanda ke suke ciki.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kara da cewa shugaba Tinubu da masu bashi shawara basu shirya gyara Najeriya ba.
Atiku ya ce gwamnatin tasu ta zo ne domin kara talauta 'yan kasar ta hanyar azurta shugabanni da iyalen su kadai ba tare da duba talakawa ba.
Atiku ya ce karin harajin VAT zai kara rusa masu sana'a da ma masana'antun kasar, inda tuni suke fama da matsin tattalin arziki tun zuwan gwamnatin Bola Tinubu.