• 17 Jun, 2025

Karin Albashi Da Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Ma'aikatan Gwamnati Baida Wani Amfani—Cewar Adams Oshiomhole

Karin Albashi Da Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Ma'aikatan Gwamnati Baida Wani Amfani—Cewar Adams Oshiomhole

1000006966.jpg

Tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole ya ce duk da karin albashi da gwamnatin Najeriya ta yi wa ma'aikata, talauci karuwa ya yi maimakon raguwa.

Oshiomhole ya ce, rashin kudin shiga mai ma'ana zai ruruta wutar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasa.

Tsohon gwamnan ya furta haka ne yayinda ya ke jawabi a wajen wani taro da cibiyar koyarda dabarun mulki ta shirya a Abuja jiya Laraba.

Oshiomhole ya kara da cewa yan kasar na cikin ukubar talauci da rashin tabbas, inda ya ce rashin albashi mai kauri da ma barazanar rasa ayyukan babbar matsalar ce a kasar.

Adams Oshiomhole wanda dan majalisar dattawa ne ya ce, ya zama dole gwamnatin Najeriya ta duba lamuran da zummar kawo canji cikin rayuwar talakan kasar.

Oshiomhole ya kara da cewa ana taka hakkin ma'aikata a Najeriya ta hanyar yi musu barazana da ma hanasu albashi idan sunyi korafi.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.