
Shafin TikTok ya ce ya goge bidiyoyi sama da miliyan 2.1 a Najeriya a cikin wata shida na farkon 2024 saboda saba ka'idojinsu.
Kamar yadda rahoton tabbatar da bin dokokin amfani da kafar da kamfanin ya fitar a ranar Talata ya nuna kamfanin ya ce ya dauki matakin ne a kokarin sa na tabbatar da samar da daidaito da kuma tsabtace kafar.
Bincike ya nuna cewa kashi 99.1 na bidiyoyin nan an cire su ne tun kafin a kawo karar su, sannan kashi 90.7 an cire su ne a cikin awa 24.
Wadannan alkaluman suna tabbatar da cewa kamfanin TikTok na hana yada abubuwa marasa kyau, domin tabbatar da samar da kafa mai kyau ga ma'abota kafar a Najeriya.
Sai dai wadannan bidiyoyin da aka goge ba su ma kai kashi daya cikin dari
na bidiyoyin da yan Najeriya suka dora a zamanin watannin da aka yi nazari domin wannan rahoton.
A duniya, TikTok ta ce ta cire sama da bidiyoyi miliyan 178 a watan Yunin 2024, inda ta ce bidiyoyi miliyan 144 daga ciki kwamfuta ce ta goge su.