
Gamayyar kamfanonin hamshakin attajirin dan kasuwan nan Abdulsamad Rabiu, wato BUA ya sanarda ribar zunzurutun kudi Naira triliyan 1.07 cikin watanni 9 kacal.
Rahoton samun ribar ya nuna kamfanin BUA ya samu cigaba daga ribar Naira biliyan 524.42 a shekarar da ta gabata zuwa 1.07 a wannan shekarar.
Kamfanin sarrafa abincin na BUA ya samu karin karfi a cikin masana'antun Najeriya musamman masu sarrafa abinci.
Habakar kamfanin na BUA ka iya bashi mataki na farko cikin kamfanonin Najeriya masu sarrafa abincin filawa a shekara mai zuwa.
Yanzu haka dai kamfanin BUA ya rantaba hannu kan yarjejeniyar kasuwanci da kasashen Turkiyya da Italiya don karfafa kasuwancin sarrafa abincin filawa.
Wani manaja a kamfanin na BUA Dakta Ayodele Abioye, ya nuna farin cikinsa kan cigaba da nasarar da kamfanin na BUA ya samu duk da dunbun kalubalen kasuwanci da ke akwai a Najeriya.