• 18 Jun, 2025

Kamfanin Mai Na NNPCL Zai Fara Jigilar Mai Daga Matatar Man Dangote Yau Lahadi

Kamfanin Mai Na NNPCL Zai Fara Jigilar Mai Daga Matatar Man Dangote Yau Lahadi

img-6393.jpeg

Kamfanin mai na NNPCL a Najeriya ya jibge tankokin mai sama da 100 a matatar man Dangote domin fara aikin jigilar mai zuwa sassan kasar.

Za a fara aikin jigilar man petur daga matatar man Aliko Dangote ne a yau Lahadi a yankin Ibeju-Lekki da ke birnin Lagos kamar yadda kamfanin na  NNPCL ya yi alkawari a baya.

Shugaban hukumar tattara harajin gwamnatin tarayya Zacch Adedeji ne ya furta hakan ranar Juma'a yayin ganawa da kwamitin shugaban kasa kan sayar da danye da tataccen mai a Najeriya.

Adedeji ya ce kamfanin mai na NNPCL shi ne zai rika jagorancin dauko mai da raba shi zuwa sassan Najeriya tare da wasu masu harkar mai a kasar.

Wannan dai babban ci gaba ne a harkar tacewa da samar da man petur a kasar ganin matatar mai na Dangote ta fara aiki batare wata matsala ba kawo yanzu.

Abin jira a gani dai shi ne dorewar wannan tafiyar ta hanyar amfanar da talakan Najeriya musamman ta fannin wadata da saukin man petur a kasar.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.