• 17 Jun, 2025

Kamfanin Mai Na NNPCL Ya Musanta Zargin Sayarda Man Fetur Mara Inganci

Kamfanin Mai Na NNPCL Ya Musanta Zargin Sayarda Man Fetur Mara Inganci

1000008942.jpg

Kamfanin mai na kasa NNPCL ya musanta zargin da ake mishi kan wani faifayin bidiyo da ke nuna kamfanin na samarda man fetur mara inganci.

Bidiyon dai ya nuna wani mutum a garin Keffi da ke Jihar Nasarawa da man fetur mara kyau, inda mutumin ya bayyana cewa kamfanin man na NNPCL ne ke samarda lalataccen man.

Mai magana da yawun kamfanin na NNPCL Olufemi Soneye ya ce, zargin ba gaskiya ba ne sakamakon binciken da suka gudanar akan batun.

Soneye ya ce, babu yadda za a yi kamfanin NNPCL ya sayarda man fetur irin wannan a kasuwa domin ba dabi'arsa ba ne, inda ya ce kamfanin NNPCL basa sayarda man fetur cikin kwalba ko jarka kamar yadda aka nuna a cikin bidiyon.

Soneye ya kara da cewa kamfanin NNPCL baida alaka da lalataccen man fetur a duk inda aka same shi a fadin Najeriya.

Olufemi Soneye ya bayyana cewar, a kullum kokarinsu shi ne samarda man fetur mai inganci a fadin duniya ba ma a Najeriya kadai ba.

Soneye ya ce, yan Najeriya su yi watsi da wannan batun saboda abu ne mara tushi da wasu marasa kishin kasa suka kirkira domin kawo rudani a harkar mai a kasar.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.