
Kamfanin mai na NNPC a Najeriya ya sanar da shirin sa na hada gwiwa da wasu kamfanoni domin fara amfani da matatun man gwamnati na kasar.
Kamfani ya ce matatar Birnin Warri da ke kudu maso kudancin kasar da matatar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya za su fara aiki domin a karkashin sabon shirin.
Hakan ya biyo bayan niyyar gwamnatin tarayya na inganta tare da bunkasa samar da wadataccen man petur a fadin kasar.
Kamfanin na NNPCL ya ce zai yi amfani da shahararrun kamfanoni wadanda suka kware wajen gyara da kulawa da matatun na Kaduna da Warri don cimma kudurin sa na kawo canji.
An gina matatar man Warri ne a shekara 1978 wacce ka iya tace gangar mai har 6,250, 000, a kowace rana.
An gina matatar ta Kaduna kuma a shekarar 1980 domin aikin tace albarkatun man kasar.
Duk da makudan kudade da gwamnatin tarayya ta kashe wajen gina matatun, rashin gwamnati mai nagarta ya tilasta durkusar da matatun batare da aikin tace koda ganga daya na mai a kasar ba.