• 18 Jun, 2025

Kamfanin Barasa A Najeriya Ta Yi Mummunan Asara Cikin Wata 9 Da Suka Gabata

Kamfanin Barasa A Najeriya Ta Yi Mummunan Asara Cikin Wata 9 Da Suka Gabata

1000004436.jpg

Kamfanin barasa a Najeriya ya fada cikin mummunar asara a cikin watanni 9 da suka shude cikin wannan shekarar.

Kamfanin ya ce, shekarar da ta gabata ta 2023 ta fi wannan shekarar ta 2024 duba da asarar da kamfanin ya yi a bana.

Kamfanin ya samu asara kwatankwacin kashi 161 a cikin kashi 200 a rahotonsa da ya fitar jiya Laraba.

Hauhawan farashin kayayyakin da kamfanin ke amfani dasu a Najeriya da rashin darajar Naira wajen kasuwancin yau-da-kullum na daga cikin dalilan da suka haddasa asarar.

Kamfanin na barasa ya kara da cewa karin kudin haraji akai-akai da gwamnatin kasar ke dorawa kamfanin shi ma babban dalili ne.

Karin haraji daga kashi 76.9 zuwa sama da haka, ya kawo karin tabarbarewar yanayin kasuwancin kamfanin a fadin kasar.

Ko kamfanin na barasa da ma sauran masana'antun Najeriya za su farfado daga tsananin matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi? ko kuma za su durkushe ne a karshe? lokaci ne kadai zai nuna hakan.

 

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.