
A kokarin gwamnatin Najeriya na kawo saukin abinci a kasar, gwamnatin ta bullo da tsarin samarda shinkafa a cikin kananan buhunan taliya domin masu kananan karfi.
Buhun shikafa yar gida dai mai nauyin 50kg ana sayarda ita ne a kan kudi Naira dubu 78 zuwa dubu 90 a kasar.
Duk da haka, kudin bai kai albashin karamin ma'aikaci ba, domin karamin albashin Naira dubu 70, yayinda har yanzu wasu jihohin kasar ba su fara biyan sabon albashin na dubu 70 ba.
Shinkafa dai a kasar na daga cikin abinci da mafi yawancin mutane birni da kauye ke muradi a fadin kasar.
Rahotanni sun nuna cewa kamfanin yin shinkafa ta Big Bull ya fara samarda shinkafar a cikin kananan buhunan domin tallafawa masu kananan karfi.
Kamfanin dai ya fara buga shinkafir cikin kananan buhunan ne kamar ta taliya akan kudi Naira 200 domin kowani dan Najeriya ya iya saya.
A watan Yulin wannan shekara, hukumar kididdiga ta NBS ta ce, kayayyakin abinci sin karu a Najeriya matuka.
Binciken hukumar ta kididdiga ya nuna farashin abubuwa da yan Najeriya ke bukata sun karu sosai tun daga watan Yunin wannan shekarar.
Hukumar ta bayyana cewa duk kayayyakin abinci kamar shinkafa da wake da tumatiri da Garri da doya da sauran abubawan rayuwa na yau da kullum sun kara kudi a kasuwa.