• 17 Jun, 2025

Jiragen Yakin Sojan Sama ANajeriya Sun Fatattaki Masu Lalata Tashar Wutar Lantarki

Jiragen Yakin Sojan Sama ANajeriya Sun Fatattaki Masu Lalata Tashar Wutar Lantarki

1000008438.jpg

Jiragen yakin sojoji sun halaka ’yan ta’adda da ke shirin kai sabon hari kan masu aikin gyaran babban layin lantarkin Arewa da ya taso daga Shiroro zuwa Kaduna da ke kokarin gyarawa.

Jiragen yakin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya sun halaka ’yan ta’adda da ke shirin kai sabon hari kan babban layin lantarkin Shiroro zuwa Kaduna da ke kokarin gyarawa.

Yan ta’addan sun gamu da ajalinsu a hannun sojoji ne a ranar Juma’a yayin da ma’aikata ke kokarin gyara babban layin lantarkin da ke dauko lantarki daga Babbar Tashar Shiroro ya raba wa yankin Arewa.

Mai magana da yawun rundunar Sojin Sama ta Nijeriya Iya Komodo Olusola Akinboyewa, ya ce an halaka su a Dajin Alawa da ke kramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.

Jihohin Arewa 17 sun shafe kwanaki 10 babu wutar lantarki a sakamakon lalacewar layin lantarkin, bayan harinda ’yan ta’adda suka kai masa.

Daga bisani Shugaba Tinubu ya umarci Minista da Manyan Hafsoshin Tsaro da Mashawarcinsa kan sha’anin tsaro su umarci dakarun su da su ba da cikakkiyar kariya ga ma’aikatan lantarki domin su gyara wutar.

Komodo Olusola Akinboyewa, ya ce, Da jiragen yakin suka yi ido da ’yan ta’addan suka bude musu wuta tare da ragargazar su da kayan aikinsu.

Ya ci gaba da cewa jiragen sun mamaye sararin samaniyar yankin da ake gyaran domin hana bata-garin sakat wajen kawo cikas ga aikin gyaran.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.