
Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce nan ba da dadewa ba zai bi sawun gwamnonin da suka fara biyan sabon albashi mafi kankanci na Naira dubu 70.
Mataimakin gwamnan jihar Manassah Daniel Jatau ne ya furta haka yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Gombe.
Shugaban ma'aikatan jihar Ahmed Kasimu Abdullahi ne ya wakilci mataimakin gwamnan inda ya bayyana cewa jin dadin ma'aikatan jihar na daga cikin abubuwan da gwamnatin Gombe ta bawa muhimmanci.
Gwamna Yahaya ya ce tuni ya kafa kwamiti da zai tabbatar da aiwatar da fara biyan sabon albashin.
Ana dai samun karin gwamnonin Najeriya da ke martaba dokar da ta umarci biyan ma'aikatan kasar sabon albashi na Naira 70,000 bayan majalisar dokokin kasar da ma Shugaba Bola Tinubu sun rattaba hannu akai.