
Jam'iyyar PDP ta gudanar da taron ta a matakin gundumomi da kananan hukumomi da ma matakin jiha a jihar Rivers, kudu maso kudancin Najeriya.
A ranar Juma'a ne wata kotu ta dakatar da jam'iyyar PDP daga aiwatar da duk wani taron zabuka a jihar amma PDP bata girmama umarnin kotun ba.
'Ya'yan jam'iyyar ta PDP dai sun hallara a sakatariyar jam'iyyar dake titin Aba a birnin Patakwal a jiya asabar don zaben wakilan jam'iyyar.
Mai Sharia Charles Wali ne ya dakatar da jam'iyyar ta PDP yin kowani irin zabe har sai kotu ta kammala sauraron karar da aka shigar a gabanta.
Mai Sharian ya umarci hukumar tsaron kasa ta DSS da sufeton 'yansandan Najeriya da kwamishinan 'yansandan jihar Rivers da ma sauran jami'an tsaro su hana jam'iyyar ta PDP gudanar da taron.