
Jam'iyyar adawa ta PDP ta dage taronta na shugabanninta da ta shirya yi gobe Alhamis.
PDP ta dage zaman taron ne domin shiryawa zaben gwamna da za a gudanar a jihar Ondo, kudu maso yammacin Najeriya ranar 16 ga watan Nuwamba.
Shugaban gwamnonin jam'iyyar gwamnan Bauchi Bala Mohammed ne ya furta haka a wata takarda da ya sanyawa hannu, bayan ya gana da wasu jiga-jigan jam'iyyar.
Taron kusoshin jam'iyyar da aka gudanar jiya Talata ya samu halartar tsofin gwamnonin jam'iyyar da sauran masu ruwa da tsaki.
PDP ta dage taron zuwa ranar 24 ga watan Nuwamban wannan shekarar domin shiryawa yadda ya kamata bayan zaben na jihar Ondo.
Jam'iyyar PDP dai wacce ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya na fuskantar matsaloli daban-daban tun bayan zaben 2023 wadanda suka hada da sauya sheka daga yayan ta da ma sauran batutuwa ciki da waje.
Abin jira a gani dai shi ne, yiwuwar warware matsalolin jam'iyyar yayinda zaben shekara ta 2027 ke karatowa.