
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta sanarda sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar jiya asabar kamar yadda ta shirya.
Hukumar ta sanarda yan takarar jam'iyya mai mulkin jihar NNPP a matsayin wadanda suka lashe zaben kananan hukumomin 44 baki daya.
Shugaban hukumar zabe na jihar Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya sanarda sakamakon zaben a hedikwatar hukumar da ke birnin Kano.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa sun gudanar da zaben kananan hukumomin ne kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada damar yin hakan.
An gudanar da zaben cikin lumana batare da tashin hankali ba cikin kananan hukumomin 44 a fadin jihar.
Hukumar zaben ta nuna farin cikinta dangane da goyon baya da masu ruwa da tsaki su ka bada domin gudanar da zaben cikin nasara.
Hukumar zaben ta mika godiyarta ga jami'an tsaro da kafafen yada labarai da kungiyoyin sa ido da yan siyasa da shugabannin addinai da matasa maza da mata bisa gudumawar da su ka bada daga farko har zuwa karshen zabukan.
Hukumar zaben ta jinjinawa mutanen jihar Kano sakamakon hadin kan da su ka bada domin wanzuwar dimukradiyya a Kano da ma kasa baki daya.