
Jam'iyyar APC mai mulki ta bukaci a gudanar da bincike kan zargin karkata tallafin abinci da gwamnatin tarayya ta aika jihar Kano.
Jam'iyyar ta bukaci a kama tare da hukunta duk wanda yake da hannu a karkata tallafin dubannin buhunan shinkafa da aka turawa Kanon domin rage radadin tsadar abinci da ake fama da ita.
Shugaban jam'iyyar reshen jihar Kano Abdullahi Abbas ya zargi wasu 'yan jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar da laifin karkata kayan abincin da gwamnatin tarayya ta bawa jihar Kano.
Abbas ya ce ya zama dole gwamnatin tarayya ta hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aikan don gujewa faruwar hakan nan gaba.
Shugaban jam'iyyar ta APC ya ce ba yau 'yan jam'iyyar NNPP a jihar Kano suke yiwa tallafin gwamnatin tarayya zagon kasa ba.