• 18 Jun, 2025

Jami'ar Jihar Osun Ta Yaye Dalibai 59 Da Sakamakon Matakin Farko

Jami'ar Jihar Osun Ta Yaye Dalibai 59 Da Sakamakon Matakin Farko

uniosun-750x536-1.jpg

Dalibai 59 ne suka gama karatun digiri na farko da matakin first class a Jami'ar jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Shugaban Jami'ar Farfesa Clement Adebooye ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a dandalin Jami'ar.

Adebooye ya ce dalibai 673 kuma sun kammala karatun digiri da matakin second class upper, inda dalibai 1,109 suka gama da matakin second class lower.

Adebooye ya kara da cewa mutane 214 ne suka kammala karatun digiri na biyu, yayin da mutum 40 suka gama karatun digirin digirgir.

Shugaban Jami'ar Clement Adebooye ya bayyana farin cikin sa da yaye daliban, inda ya yi alwashin zai maida Jami'ar cibiya mai nagarta a Najeriya da ma duniya baki daya.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.